Afirka ta Kudu na neman gafarar Najeriya

A

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da aka samu, kuma ta ce tana daukar kwararan matakai

Afirka ta Kudu ta nemi gafarar Najeirya a kan hare-haren kin jinin bakin da aka kai wa ‘yan Najeriya da ke kasar.

Jakada na musamman na gwamnatin Afirka ta Kudu, Jeff Radebe, ya gabatar da takardar neman afuwar a madadin Shugaba Cyril Ramaphosa, a wata ganawa da yi da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Da alamu gwamnatin Afirka ta Kudu na kokarin kyautata alakarta da sauran kasashen Afirkan wadanda hare-haren kin jinin baki a Afrika ta Kudun ya shafa.

Jami’in na Afirka ta Kudu, ya shaida wa shugaba Buhari a Abuja cewa gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da aka samu, kuma ya ce tana daukar kwararan matakai.

A yayin da Afirka ta Kudu ta dauki wannan mataki, Najeriya na ci gaba da kwashe ‘yan kasarta daga Afirka ta Kudu.

Ana sa ran isowar wani rukuni na ‘yan Najeriya 319 daga Afirka ta Kudu a filin jirgin sama da ke Legas a ranar Talata.

Sai dai Shugaba Buhari ya tabbatar wa jami’in cewa za a kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...