Afghanistan: Bam ya kashe yara tara a hanyarsu ta makaranta | BBC news

Police in Afghanistan

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Bam ya kashe wasu yara tara kan titi a arewa maso gabashin Afghanistan a hanyarsu ta zuwa makaranta.

An bayyana cewa yaran – maza tara da mace daya wadanda ke tsakanin shekaru bakwai zuwa 10, a rashin sani suka taka wata nakiya da aka dasa, kamar yadda jami’ai a kasar suka shaida.

Har yanzu, babu wata kungiya da ta fito fili ta dauki nauyin dashen wannan nakiyar.

Ko a watan Oktoba, sai da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an kashe fararen hula 1,174 cikin watanni uku kafin Satumba.

Mai magana da yawun gwamnan lardin Takhar Jawad Hejri, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ”da misalin karfe 8.30 na safe, yara tara sun mutu sakamakon wata nakiya da aka dasa wadda ta fashe bayan sun taka.”

Ya zargi ‘yan kungiyar Taliban da dasa nakiyar.

Kungiyar ta Taliban ta kwace iko da lardin Takhar makonni da dama da suka wuce kafin sojojin Afghanistan suka fatattake su.

An bayyana cewa al’adar kungiyar Taliban ne dasa irin wadannan nakiyoyi a lokacin da ake fatattakar su daga gari inda suke da niyar harin sojojin da ke biye da su.

Kungiyar dai ba ta ce komai ba dangane da lamarin.

Ko a watan Mayun bana, sai da irin wannan nakiyar ta kashe yara bakwai da raunata biyu a kudancin lardin Ghazni.

Haka zalika a watan Fabrairu sai da yara bakwai suka rasa ransu 10 kuma suka raunata bayan da wani makamin roka ya fashe yayin da suke wasa da shi a lardin Laghman.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...