Adadin Masu Coronavirus a Najeriya Ya Doshi 5000 | VOA Hausa

Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta NCDC ta fitar, sun yi nuni da cewa mutum 146 sun sake kamuwa da cutar cikin yinin jiya Talata.

Har yanzu dai Legas ce ke kan gaba wajen samun yawan masu dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabin mutum 57.

Baya ga Legas, jihar Kano wacce ta ke fama da yawan mace-mace a ‘yan kwanakin nan ita ma ta samu mutum 27 da suka kamu da cutar.

Ya zuwa yanzu adadin masu cutar ya kai 4,787 a duk fadin kasar.

Adadin masu rasuwa sakamakon cutar shi ma yana dada haurawa, inda a cikin yinin jiya kawai aka samu mutum 8 da suka mutu sakamakon cutar.

Hakan ya mayar da adadin wadanda coronavirus ta kashe zuwa 158.

Masu samun waraka su ma sun kara yawa, inda yanzu Najeriya ke da mutum 959 da suka warke daga cutar.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...