Abun da shugaba Buhari ya je yi a London

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin London

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sake yin bulaguro zuwa birnin London bayan kammala taron kasuwanci na duniya na yini uku a birnin Riyadh na Saudiyya.

A ranar Asabar ne Shugaba Buhari ya bar kasar Saudiyya zuwa Birtaniya, daga nan ya dawo Najeriya.

Fadar shugaban ta ce ya tafi London ne bisa radin kansa, ba tare da cikakken bayani ba, duk da ce-ce-ku-ce kan yawan tafiye-tafiyensa.

Shugaban ya ziyarci kasashen Japan da Rasha da Afirka ta kudu da kuma Amurka kafin ya tafi zuwa Saudiyya.

Babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta ce ‘babu wata riba da kasar ta samu’ daga yawan tafiye-tafiyensa zuwa kasashen waje.

Sai dai fadar shugaban ta ce kimar shugaban da darajarsa a idon kasashen duniya ne ya sa ake yawan halartarsa taro kuma tafiye-tafiyensa suna da muhimmaci ga ci gaban kasar.

Ana sa ran Shugaba na Najeriya zai dawo Abuja a ranar 17 ga watan Nuwambar 2019.

Idan har Buhari ya koma zai kasance kwanaki 425 ke nan shugaban ya yi a kasashen waje a tsawon shekara hudu da rabi na mulkinsa.

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Image caption

Buhari ya yi Umrah a Makkah kafin ya mika zuwa London

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...