Abubuwan da suka faru a lik É—in Firimiya

Fermino da sauran 'yan wasan Liverpool na murnar bal din da ya ci

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwallayen da Roberto Firmino da Sadio Mane suka ci su suka ba wa Liverpool maki uku

masu rike da kofin Zakaran Zakaru na Turai Liverpool sun ci gaba da samun nasara a kakar da aka shiga inda suka yi galaba a gidan Southampton, St Mary da ci 2-1 a wasan mako na biyu na Premier.

Sadio mane ne ya fara daga raga a wasan da kungiyar ta Jurgen Klopp ta yi nasara da ci 2-1, bayan da daman ya ciu biyu a karawar da Reds din suka doke Chelsea a fanareti a Istanbul ranar Laraba.

Roberto Firmino ya kara ta biyu, kafin kuma golan Liverpool din Adrian ya tafka kuskuren da ya ba wa Danny Ings damar zare daya bayan wasan ya yi nisa an kusa tashi.

Zakarun gasar ta Premier kuwa Manchester City a karon farko tun watan Disamba na 2018 sun barar da maki biyu a gida, bayan da suka yi canjaras 2-2 da Tottenham.

‘Yan City din sun ga samu sun ga rashi bayan da na’urar bidiyo mai taimaka wa alkalin wasa, ta nuna cewa bal din da Gabriel Jesus ya ci a daidai lokacin tashi daga wasan ba halartacciya ba ce.

Tun a kashin farko na wasan Raheem Sterling ya ci wa City bal din farko, amma nan da nan ba tare da bata wani lokaci ba Erik Lamela ya farke ta.

Sergio Aguero ya kara ci wa City ta biyu, kafin kuma Lucas Moura ya rama, bayan da ya yi canji ya shigo.

Teemu Pukki ya samu rana inda ya ci uku rigis, a wasan da bakin Premier, Zakarun gasar Championship na kakar da ta wuce Norwich City suka farfado daga kashin da suka sha na wasansu na farko a hannun Liverpool, suka casa Newcastle United 3-1.

Dan wasan gaban na Finland wanda yanzu ya ci bal hudu a wasa biyu na Premier, ya fara daga raga ne tun a kashin farko na wasan, kafin kuma ya kara biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Jonjo Shelvey ya ci wa kungiyar ta kociya Steve Bruce, Newcastle United, ladan gabe daya.

Aston Villa kuwa za ta ci gaba da jiran lokacin da za ta yi nasararta ta farko ta kakar nan, bayan da ta yi rashin nasara a gidanta da ci 2-1, a hannun Bournemouth.

Fanaretin da Joshua King ya ci a minti biyu na wasan, da kuma kwallon farko da dan wasan Liverpool da ya tafi aro Harry Wilson ya ci ta ba wa bakin na kociya Eddie Howe damar kankane wasan tun da farin-farko.

Sai dai Douglas Luiz ya motsa masu masaukin bakin da bal daya da ya farke musu a kashi na biyu na wasan.

Dan wasan na Brighton ta saya da bazara Leandro Trossard ya farke kwallon da Javier Hernandez ya fara daga raga da ita, a wasan da aka tashi 1-1 da West ham a filin wasa na Amex Stadium.

Tun da farko na’urar bidiyo mai taimaka wa alkalin wasa ta nuna cewa bal din da Trossard ya fara ci a kashin farko na wasan , ya yi satar gida, amma kuma ya samu damar farkewa wadda Hammers din suka fara ci a minti na 61.

Ita kuwa Everton kwallon da Bernad ya ci a minti na goma da wasa, ita kadai take bukata ta yi nasara a gida tsakaninta da tsohuwar kungiyar kociya Marco Silva, Watford.

A ranar ta Asabar, tun da farko a karawar da aka yi a filin Emirates bal din da Pierre-Emerick Aubameyang ya ci ta ba wa Arsenal damar galaba a kan Burnley da ci 2-1.

Tun da farko Gunners din ke kan gaba bayan da Alexandre Lacazette ya ci mata bal dinsa ta farko bayan ya dawo daga jinya, amma kuma Ashley Barnes ya farke wa bakin kafin tafiya hutun rabin lokaci.

A ranar Lahadi kuwa wasanni biyu ne za a yi a gasar ta Premier, inda sabbin zuwa Sheffield United za su karbi bakuncin Crystal Palace a wasansu na farko na gida da karfe 2:00 na rana agogon Najeriya.

Ita kuwa kungiyar kociya Frank Lampard, Chelsea za ta nemi kauce wa rashin nasara a karo na uku a jere a cikin kwana takwas a wasan da za ta karbi bakuncin Leicester City a Stamford Bridge da karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...