Abubuwan da Buhari ya tattauna da shugaban INEC

Shugaban Najeriya Muhammadu BUhari tare da shugaban hukumar zaben kasa INEC Mahmoud Yakubu da babban sipeton 'yan sanda Muhammad Adamu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci hukumar zaben kasa INEC ta tabbatar da yin adalci a zabukan cike gurbi da za a yi a watan Janairu da kuma na nan gaba.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da shugaban hukumar zaben kasar Mahmoud Yakubu da Supeton ‘yan sanda Muhammad Adamu, wadanda suka je domin yi masa karin bayani dangane da yadda zabukan 2019 suka kasance da kuma shirin da aka yi na karasa wasu da ba a kammala ba a watan Janairu.

A sanarwar da mai taimakawa shugaban kasar ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya fitar, shugaba Buhari ya bukaci INEC ta tsaya kaida fata wajen yin adalci da kuma bin doka a dukkanin zabukan da zata gudanar, ta yadda ‘yan Najeriya da ma duniya baki daya zasu yi amanna da ingancin zabukan.

“Dole ne kowanne dan Najeriya ya samu damar zabar duk wanda yake so ba tare da fuskantar wani kalubale ba” Inji shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan dai na zuwa ne bayan kammala zabukan jihohin Kogi da Bayelsa, da kungiyoyin masu sanya ido na ciki da wajen kasar suka ce an tafka magudi da keta doka a cikin sa.

‘Yan adawa sun ce ba abin da zai sauya a zabukan cike gibin da za a gudanar.

Injiniya Buba Galadima daya daga cikin manyan masu hamayya da gwamnatin APC ya ce “shugaban ya sha fadar za a yi zaben adalci amma abin da ya faru a Kogi da Bayelsa ya nuna ba abin da zai sauya.”

Sai dai a nata bangaren hukumar zaben kasar ta ce tana bakin kokarinta wajen tabbatar da ganin ana samun ci gaba a zabukan kasar.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...