Abu 10 da aka ambato a zaman jin bahasin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska

Abin da ya sa majalisun dokokin Najeriya suke son yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska

Batun yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska abu ne da har yanzu ke jan hankali a ƙasar, kodayake galibin masu tsokaci na ganin lokaci ya yi na sauya ko yin gwaskwarima ga kundin.

Akasarin wadanda suka tafka muhawara da bayar da bahasi a zaman da majalisar dokoki ta shirya na kwana biyu a sassan kasar na son ganin an aiwatar da sauye-sauye a kundin 1999.

Daga cikin manyan batutuwan da zaman ya mayar da hankali a kansu akwai maganar sakar wa ƙananan hukumomi da ɓangaren shari`a mara, akwai batun sake fasalin ƙasa da batun samar da ƴan sanda jihohi.

Jihohin da aka yi wannan zama irinsu Kaduna da Asaba da Enugu da Akure, sun yce bai kamata a ce majalisa ce za ta jagoranci gudanar da sauye-sauyen ba, suna mai cewa taron zai kasance tamkar zaman shan shayi.

Ga dai abubuwa 10 da suka biyo bayan zaman neman yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska:

1. An gaggauta shirya kundin tsarin mulki na 1999 – Gwamnan Delta

Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce samar da sabon kundin tsarin mulki yana da muhimmanci sosai la’akari da giɓin da aka bari a kundin 1999.

Gwamnan ya nuna cewa an yi gaggawar samar da kundin tsarin mulki a 1999, kuma ko da an amince da kwaskwarimar akwai wasu gyare-gyare da ba lallai a sauya ba.

2. Kundin da ake bi a yanzu na taka rawa wajen neman wargaza Najeriya, in ji Afe Babalola

Ɗaya daga cikin dattijan jihar Ekiti, wanda kuma ya samar da jami’ar Afe Babalola, Aare Afe Babalola, ya ce yunƙurin majalisa na yi wa kundin 1999 gyaran fuska ba zai yi tasiri ba.

Ranar Laraba Babalola ya ce abin da ya kamata majalisa ta yi shi ne “kiran taron ƙasa domin tattauna sabon kundin tsari da zai samar da tsarin gwamnati mai Firaiminista”.

Sannan ya kuma ce, “me zai hana majalisa ta kira zaɓen raba-gardama kan zaɓi tsakanin kundin 1999 da na 1963”.

3. Bukatar neman samar da sabon kundin mulki ƙoƙari ne na haifar da ruɗani – Ekweremadu

A lokacin da yake jawabi, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu, ya ce masu ruruta batun samar da sabon kundin tsarin mulkin Najeriya na neman haddasa rikici da ruɗani ne.

Ekweremadu ya ce ya ji ana ta tafka muhawara; wasu na cewa a dawo da tsohon kundin tsarin mulkin 1960, wasu na cewa na 1963, wasu na yin na’am, to me ya sa ba za a watsar da su ba a kawo sabon kundi?

“Tambayar a nan ita ce ta yaya hakan zai samu? Babu wannan tsarin a kundi tsarin mulkin indai ba ruɗani ake son haifarwa ba,” in ji Ekweremadu.

4. Gwamnatin tarayya na daukan nauyin da yafi ƙarfinta, in ji El-Rufai

Masu ruwa da tsaki daga jihohi hudu na arewa maso yammacin Najeriya wato Kaduna da Katsina da Kano da Jigawa duk sun hallara a Kaduna domin ba da bahasinsu.

Gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai, ya ce rage karfin ikon gwamnatin tarayya na da muhimmanci saboda tsarin da ake bi a yanzu ayyuka sun yi wa gwamnatin tarayya yawa wanda hakan ke tasiri wajen ayyukanta.

Gwamnan ya kuma ce “ya kamata mu tantance irin yadda ya kamata tsaron ƙasarmu ya kasance da ci gabanta da kuma ci gaban al’ummarmu”.

5. Kundin 1963 shi ne mafi dacewa da Najeriya – Akeredolu

Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu na da ra’ayin cewa kamata ya yi a dawo da amfani da kundin tsarin mulkin 1963, wanda ke kunshe da tsarin federaliya na ƙwarai.

Gwamnan ya soki kundin tsarin mulkin 1999, yana mai cewa akwai rashin dacewa kuma ya kamata a ce tuni an sauya shi.

Sannan yana mai gargaɗin cewa gaɓar da ake a yanzu na neman yiwa kundin 1999 kwaskwarima ba batu ne da za a yiwa rikon sakainar kashi ba.

6. Legas ta nemi a bata matsayi na musamman

Shi kuwa anasa ɓangaren gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya buƙaci a basu matsayi na musamman a tattalin arziki, yana mai cewa ci gaba da nasarorin da ake gani a Najeriya nada alaƙa da irin ci gaba da nasarorin da Legas ta samu.

Gwamnan ya kuma goyi-bayan kafa rundunar ƴan sanda jihohi da kuma rungumar tsarin federaliya a Najeriya.

7. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci tsarin federaliya na haƙiƙa da sauya fasali

Shugaban ƙungiyar ƙwadago Ayuba Wabba, ya jadada bukatunsu a fanin albashi mafi ƙanƙanta, kazalika ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ita ma ta gabatar da bukatunta ga kwamitin majalisar dattawan da ke zama a Kaduna, inda ta jadada buƙatar sakar ma ƙananan hukumomi mara.

Hakazalika shugaban ƙungiyar CAN, Rev Steven Adegbite ya nemi bayyani kan kafa kotunan shari’a tunda kundin tsarin ya ce babu addini a jihohi.

8. Akwai buƙatar ƴan aware su rungumi sulhu – Yahaya

Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bukaci masu neman ɓallewa su bai wa majalisa dama su gyara kura-kuran da ke cikin kundin 1999, yana mai cewa sulhu shi ne abu mafi dacewa.

Yahaya da ke shaida haka a zaman arewa maso gabashi da ake yi a jiharsa, ya bukaci masu kalaman ƙiyayya su nesanta kansu da ambatar abubuwan da ke rura wutar rikici yana mai cewa sulhu shi ne mafi alheri ta hanyar fuskantar gyaran da ake bukata a kundin tsarin mulkin 1999.

9. Ba ma goyon-bayan kafa ƴan sandan jaha – Gombe

Sai dai Antoni-Janar kuma kwamisinan shar’a a Gombe, Zubair Umar, ya ce akwai rashin dacewa a ce jihohi na neman kafa rundunar ƴan sanda jiha saboda rashin kuɗaɗe.

Kalaman kwamishinan akan adawa da kafa rundunar ya ja hankali tsakani masu sauraron yada ake karbar bahasi.

Ya kuma ƙara da cewa ba sa goyon-bayan tsarin ne saboda matsalolin kudi da ake ciki a jihohi, wanda ba zai bada damar nuna goyon-baya ga kafa rundunar jiha ba.

A jihar Sokoto kuma batun bai wa ɓangaren shari’a cikakken yanci da daidaiton jinsi da sake fasali da rawar da sarakunan gargajiya za su iya takawa su suka ja hankalin tattaunawar.

10. Gyaran kundin tsari ba zai kawo zaman lafiya ba, in ji Lalong

Ana shi martani, gwamnan Plateau kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa, Simon Lalong, ya ce haɗin-kan Najeriya ba shi da alaka da sauya kundin tsarin mulki ko da kuwa za a sauya kundin bil adadin.

“Inda ana son ganin c igaba da zaman lafiya da shugabanci mai kyau to dukkanin wadanan sun ta’alaka ne kan irin rawar da ƴan kasa ke takawa wajen amfani da biyayya ga kundin tsrain mulki, in ji Lalong.

Gwamnan da ke shaida hakan a Plateau a sauraron bahashin tsakiyar Najeriya, ya ce kowanne ɗan ƙasa na da rawar da zai taka wajen mutuntawa da kare kudin tsarin mulkin ƙasa.

A kan batun sake fasalin ƙasa, Lalong ya ce lokaci ya yi da ya kamata a fuskanci hakan da tabbatar da cewa kiraye-kirayen da zakuwar da ake nunawa an shawo kan su.

Ƙarin haske

A wannan Larabar aka kammala zaman karbar bahasin na kwanaki biyu da ke jin ra`ayoyin jama`a game da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar ke yi.

Ana dai jima ana samun korafe-korafe kan wasu gyare-gyare da ake gani da jimawa ya kamata a aiwatar da su.

Sai dai yayin da wasu ke maraba da wasu batutuwan da aka gabatar, akwai masu adawa da ganin yanzu ba lokaci ba ne na neman sauyi a kundin la’akari da wasu tarin batutuwan da ke addabar ƙasar.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...