Abinda ya kamata ku sani kan wasan PSG da Man City

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta ziyarci Paris St Germain, domin buga wasa na biyu na cikin rukuni a Champions League ranar Talata.

Wannan shine wasa na shida da kungiyoyin biyu za su fafata a gasar ta kofin Zakarun Turai, inda City ta ci karawa uku da canjaras biyu.

City ce ta doke PSG 4-1 gida da waje a wasan daf da karshe a bara a gasar ta Zakarun Turai,

Kungiyoyi biyun za su buga wasannin da kwarin gwiwa, bayan da PSG ke kan teburin Ligue 1 da cin dukkan wasanninta takwas a kakar bana, ita kuwa Manchester City ta je Stamford Bridge ta doke Chelsea a gasar Premier League ranar Asabar.

Sai dai PSG bata ci wasa ba a karawa hudu a Champions League, tun bayan canjaras da Club Bruges a wasan zagayen farko.

City ta casa RB Leipzig 6-3 a gida a wasan farko a cikin rukuni a bana, kuma ta yi karawa 10 ba tare da an doke ta ba a Champions League.

Wasanni biyar baya da suka kara tsakanin PSG da City:

Champions League Talata 4 ga watan Mayun 2021

  • Man City 2 – 0 Paris St-Germain

Champions League Ranar Laraba 28 ga watan Afirilun 2021

  • Paris St-Germain 1 – 2 Man City

Champions League Ranar Talata 12 ga watan Afirilun 2016

  • Man City 1 – 0 Paris St-Germain

Champions League Ranar Laraba 6 ga watan Afirilun 2016

  • Paris St-Germain 2 – 2 Man City

UEFA CUP Ranar Laraba ga watan Disambar 2008

  • Man City 0 – 0 Paris St-Germain

‘Yan wasan PSG da za su kara da Man City:

28.Eric Junior Dina Ebimbe

Asalin hoton, Getty Images

PSG ta bayyana Messi cikin wadanda za su fafata da City a Faransa, karon farko da zai buga Champions League a kungiyar, wanda bai yi mata wasa biyu a League 1, sakamakon jinya da ya yi.

Kyaftin din Argentina, wanda ya taka leda karkashin Pep Guardiola a Barcelona bai ci kwallo ba har yanzu a wasa uku da ya buga wa sabuwar kungiyarsa.

Messi shine kan gaba da ya ci Manchester City kwallaye da yawa – wanda ya zura shida a wasa hudu, har da guda hudun da ya ci City a karawa da Barcelona da biyu a lokacin da kocin yake Bayern Munich.

(BBC Hausa)

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...