Abin Da Masu Sharhi Ke Cewa Kan Matsayar Gwamnonin Arewacin Najeriya Game Da Mulkin Karba-Karba

A yayin taron hadin gwiwa da sarakunan gargajiyar yankin da ya gudana a jihar Kaduna, gwamnonin arewacin Najeriya 19 suka bayyana matsayarsu game da batun tsarin karba-karba da wajibcin maida shugabancin kasar zuwa kudanci batun da a baya suka ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

Yankin kudancin kasar na fadin ya zama wajibi shugbancin kasar ya koma bangarensu, yayin da wasu daga cikin shugabannin Arewa ke cewa kundin tsarin mulki bai tsara hakan ba.

Gwamnan jihar Filato, Samon Lalong ya ce yayin da wasu gwamnonin Arewa ke ganin lokaci ya yi a mayar da mulki kudu, amma taron da shugabannin suka gudanar sun yanke shawarar cewa hakan ya sabawa tsarin mulkin Najeriya, domin tsarin mulki bai tilastawa kowa ya yi zabe ba.

Barrista Mainasara Kogo Umar, ya ce maganar karba-karba batu ne na san rai amma taken Najeriya ya bayyana cewa hadin kan kasa da girmama bangarori daban-daban shi ne zai kawo ci gaban al’umma.

A wani bangaren kuma wasu na ganin duk da cewa mulkin na karba-karba ba ya cikin kundin tsarin mulki, tsarin zai iya samar da daidaito wajen samar da zaman lafiya da kore rarrabuwar kawunan al’umomin kasar.

A ‘yan watannin baya kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya suka yi taro a jihar Legas inda suka cimma matsaya cewa shugabanicn kasar ya koma yankinsu.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...