‘Yan bindiga sun sake kaddamar da hare-hare a wasu kauyukan jihar Katsina ta shugaba Muhammadu Buhari bayan kashe mutum sama da 20.
An kai hare-haren ne ranar laraba a kauyukan Dan Tsunsu da Na huta da kuma ‘yan Kura da ke cikin karamar hukumar Safana a ranar Laraba, kamar yadda wani mazauni yankin ya shaida wa BBC.
Babu karin bayani game da adadin mutanen da aka kashe a hare-haren ko daga bangaren rundunar ‘yan sanda.
Wannan na zuwa bayan hare-haren da aka kai wasu kauyuka a Batsari da Dan Musa da kuma Faskari, inda aka kashe mutum sama da 20.
Batun kashe-kashe mutane na neman zama ruwan dare a Najeriya, duk kuwa da ikirarin gwamnati da jami’an tsaro na kawo karshen matsalar da yanzu ta addabi yankin arewa maso yammacin kasar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce shugaba Buhari ya umarci babban sufetan ‘yan sandan kasar da kuma babban hafsan soji su tura tawaga zuwa jihar da gaggawa tare da dawo masa da bayani.
Wannan na zuwa ne bayan wata zanga-zanga da wasu ‘yan jihar suka yi dauke da gawawwakin wasu da aka kashe domin nuna bacin ransu da tabarbarewar tsaro a jihar.
A hirarsa da BBC, Malam Garba Shehu ya ce shugaban ya bukaci tawagar da aka tura zuwa Katsina ta bayyana dalilin da ya sa matsalar ta ki ci ta ki cinye wa.
“Menene matsalolin da ake fuskanta, shin matsalar ta shafi rashin kudi ne, ko kayan aiki ko matsalar jami’ai ce,” in ji shi.
Rahotanni sun ce Buhari ya gana da gwamnan Katsina Aminu Bello Masari a fadarsa a ranar Laraba kan matsalar tsaron a jihar.
An dai dauki lokaci ana kisa da satar mutane a jihohin Zamfara da Katsina, lamarin da ya sa wasu ke dora laifin ga sakacin gwamnati na rashin daukar matakin da ya kamata tare da sauke hakkin kare rayuka da dukiyar al’umma da ya rataya a wuyanta.