
Ɗantakar jam’iyyar APC a zaɓen sanatan Kano ta tsakiya, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya shigar da ƙara a kotun sauraron kararrakin zabe dake Kano inda yake kalubalantar nasarar da Rufa’i Sani Hanga ya samu na jam’iyyar NNPP.
Zaura ta hannun lauyansa, Ishaka Dikko ya roki kotun da ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashen zaɓen kana ta jingine sanarwar da hukumar zaɓe ta INEC ta yi da baiwa Hanga nasara.
Ya yi zargin cewa zaɓen sanatan Kano ta tsakiya na cike da kura-kurai da kuma saɓa ka’idar dokokin zaɓe.
Amma kuma a martaninsu hukumar zabe ta INEC, Hanga da jam’iyar NNPP sun dage cewa an yi zaɓen kamar yadda dokar zabe ta shimfida.
