A Mako Biyu Sojoji Sun Lalata Haramtattun Matatun Mai 41 A Yankin Neja Delta

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce sojojin rundunar Operation Delta Safe sun samu nasarar lalata haramtattun wuraren da ake tace ɗanyen man fetur guda 41 a cikin makonni biyu.

A yayin wata ganawa da yan jaridu a ranar Alhamis, Kanal Musa Danmadami daraktan yaɗa labarai ya ce an kuma samu nasarar kwato lita miliyan 1.06 na ɗanyen mai.

Ya ce tukunyoyin dafa mai 156 da tankuna 189, ramuka 12 da kuma jiragen ruwa na katako 150 aka lalata a yayin farmakin.

Danmadami ya ce waɗanda ake zargi da laifi 18 aka kama a yayin da aka kwace motoci 6, litar man gas 13500 da kuma ta manfetur 8500.

More from this stream

Recomended