A dakatar da maganar zaɓen ‘yar tinƙe a yanzu – Attahiru Jega

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta INEC a Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya faɗa wa Majalisar Dokoki cewa yin amfani da ƙarfin ikonsu wajen sanya wa sabuwar dokar zaɓen hannu “ba shi ne zaɓi mafi dacewa ba”.

Farfesa Jega ya bayyana haka ranar Lahadi yayin wani taron ‘yan ƙasa kan Ƙudirin Dokar Zaɓe na 2021 wanda cibiyar Yiaga Africa ta shirya, inda ya nemi a dakatar da zaɓen ‘yar tinƙe tukunna wanda dokar ta tanada.

A cewarsa, Najeriya za ta fi samun natsuwa idan ta gudanar da zaɓe da sabuwar dokar zaɓe “saboda za ta kyautata ingancin zaɓukan da kuma shirye-shiyen gudanar da su”.

Ya ce: “Game da zaɓen ‘yar tinƙe, tabbas harkokin zaɓe za su fi inganta idan muka yi amfani da ‘yar tinƙe ta hanyar da ta dace. ‘Yan majalisa sun sani cewa gwamnoni na yin yadda suke so da zaɓe ta hanyar wakilai saboda haka suka yi tunanin idan aka koma yin ‘yar tinƙe za su samu ‘yanci.

“Sai dai ya kamata mu duba yanayin nan da kyau…hanya mafi sauƙi ba ita ce tsallake Shugaba Buhari ba, a dakatar da maganar ‘yar tinƙe tukunna har sai mun tabbatar jam’iyyu za su iya gudanar da irin wannan zaɓen.”

Wasu ‘yan majalisa sun yi barazanar cewa za su amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba su don saka wa dokar hannu bayan Buhari ya ƙi yin hakan, yana mai cewa “dole ne a bai wa ‘yan ƙasa zaɓi fiye da zaɓen ‘yar tinƙe kawai”.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...