Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudin zaben 2019

Sanata Bukola Saraki


Majalisar ta kara naira biliyan 45.5 a kan naira biliyan 189 da kwamitin majalisar kan INEC ta gabatar da farko

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudi na naira biliyan 189 wanda hukumar zabe zata yi amfani da shi don ayyukan zaben da za a gudanar a 2019.

Sai dai majalisar dattawan ta ki amicewa da kasafin kudin jami’an tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika masu ranar Laraba.

Sanata Ahmad Lawan ya shaida wa BBC cewa “a yanzu kwamitocin majalisar na kudi da na kasafin kudi na aiki kan tantance kasafin kudi da Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a bai wa jami’an tsaro don amfani da shi a zaben badi.”

Ya kuma ce su na sa rai zuwa mako mai zuwa ne majalisar za ta amince da kasafin kudin jami’an tsaron.

  • Shin me Buhari ya fada wa shugabannin Majalisa?
  • ‘Yanzu PDP ta fi APC karfi a majalisar dattawa’

Haka kuma, Majalisar ta kara naira biliyan 45.5 a kan naira biliyan 189 da kwamitin majalisar kan INEC ta gabatar da farko.

Majalisar dai ta amince da kasafin kudin ne bayan da shugaban kwamitin kasafin kudi, Danjuma Goje ya mika rahoton da kwamitin nasa ya hada bayan duba wasikar da Shugaba Buhari ya aika wa majalisar.

Ranar Laraba ne dai shugaban ya rubuta wa majalisar dattijan, inda ya bukaci su amince da naira biliyan 242 kamar yadda hukumar INEC da hukumomin tsaro su ka bukata don gudanar da zabukan 2019.

More from this stream

Recomended