Majalisar dokokin jihar Kano ta sahalewa gwamna Abba Yusuf ya naɗa kwamishinoni biyu


Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance tare da amincewa da naɗin Sanusi Ahmad Bature da Balarabe Sa’idu Gani a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwa ta jihar.

Kafin tantance shi a yayin zaman majalisar Sanusi Ahmad Bature shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf a yayin.da Balarabe Sa’idu Gani  ya kasance tsohon kakakin majalisar dokokin jihar.kuma tsohon Kakakin Majalisar Dokokin jihar.

Bature, wanda ya shafe fiye da mintuna 30 yana amsa tambayoyin ‘yan majalisar yayin tantancewar, ya ce zai ba da muhimmanci wajen farfaɗo da jaridar gwamnatin jihar mai suna dake kira da Triumph da sauran kafafen yaɗa labarai mallakin gwamnati.

Ya kuma yi alƙawarin tallafa wa kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu domin tabbatar da dorewarsu da ci gabansu.

Haka kuma, Balarabe Gani wanda ya taba zama kakakin majalisar dokokin jihar kano a lokacin mulkin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, shi ma an tantance shi tare da amincewa da naɗinsa.

Bayan kammala tantancewar, Gani ya nuna godiyarsa bisa damar da aka ba shi, tare da alƙawarin mara wa gwamnatin jihar baya wajen aiwatar da ayyukan ci gaba da kuma tabbatar da amfanin dimokuraɗiyya ya isa ga al’ummar Jihar Kano.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...