
Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta gabatar da shawarar samar da ƙarin kujeru 74 na musamman ga mata a Majalisar Dattawa da ta Wakilai, tare da ware kujeru uku ga mata a kowace Majalisar Dokokin Jihohi 36, domin ƙara yawan mata a harkokin siyasa da shugabanci a Najeriya.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a wajen taron makon shari’a na shekarar 2026 da ƙungiyar lauyoyin mata ta ƙasa (FIDA), reshen Jihar Ekiti, ta shirya.
Taron ya gudana ne ƙarƙashin taken, “Adalci a Duniyar da ke Sauyawa: Magance Sabbin Ƙalubalen da ke Shafar Mata da Yara.”
Bamidele, wanda ke wakiltar mazabar Sanatan Ekiti ta Tsakiya, ya ce gyaran kundin tsarin mulkin da ake shirin yi na da nufin kawar da matsalolin da ke hana mata shiga harkokin mulki, tare da samar da tsarin siyasa mai bai wa kowa dama.
Ya bayyana cewa shirin na cikin aikin da kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ke gudanarwa, kuma ba zai cire ko maye gurbin kujerun da sauran zaɓaɓɓun wakilai ke kai a halin yanzu ba.
A cewarsa, idan aka amince da shawarar, za a ƙara kujeru 37 a Majalisar Dattawa da wasu 37 a Majalisar Wakilai, ta yadda kowace jiha da Babban Birnin Tarayya Abuja za su samu ƙarin kujera ɗaya a kowace majalisa.
Bamidele ya ce kwamitin ya kuma gabatar da shawarar ƙara kujeru uku na musamman ga mata a kowace Majalisar Dokokin Jihohi, inda ya bayyana cewa za a gudanar da tsarin na tsawon shekaru 16, wato zangon zaɓe huɗu, kafin a sake nazarinsa.
Ya ce wannan wa’adi zai ba da damar tantance tasirin shirin wajen ƙara yawan mata a harkokin siyasa da kuma samar da al’adar siyasa mai bai wa kowa dama.
Sanatan ya jaddada cewa shirin ba na wata jam’iyya ba ne, illa wani mataki na kundin tsarin mulki da aka tsara domin magance wariya da rashin wakilcin mata a harkokin yanke shawara.
Ya kuma bayyana cewa kwamitin ya fara tattaunawa da majalisun dokokin jihohi, domin amincewarsu na da matuƙar muhimmanci wajen kammala gyaran kundin tsarin mulkin.
A cewarsa, shirin ya samu goyon bayan wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu.
Bamidele ya kuma jaddada muhimmancin samar da dokokin da za su kare mata, yara da masu nakasa, musamman ta fuskar samun kiwon lafiya, ilimi da tallafin jin ƙai.
Ya ce dole ne a tabbatar da cewa waɗanda ke fuskantar cin zarafi suna samun damar neman adalci cikin sauƙi, ba tare da tsoratarwa ko nuna musu wariya ba.
Ya ba da misali da mata masu fuskantar cin zarafin cikin gida, da kuma yaran da ake cin zarafinsu, yana mai cewa ya kamata a ba su kariya, kulawar lafiya da taimakon shari’a, yayin da ake hukunta waɗanda suka aikata laifuka bisa doka.
Ya kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin majalisa, bangaren zartarwa, kotuna, jami’an tsaro, ƙungiyoyin addini, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin farar hula domin inganta kariyar mata da yara.
A nata jawabin, mataimakiyar shugabar jami’ar Afe Babalola da ke Ado-Ekiti, Farfesa Smaranda Olarinde, ta yi kira da a samar da ingantattun dokoki da tsare-tsare domin kare mata da yara daga sabbin nau’o’in cin zarafi.
Ta ce bunƙasar fasahar basirar ɗan Adam (AI) da kafafen sadarwa na zamani sun haifar da wasu sabbin barazana, ciki har da bibiyar mutane ta intanet, cin zarafi a kafafen sada zumunta, ƙirƙirar hotunan bogi ta amfani da fasaha (deepfake), kwaikwayon wasu mutane da kuma cin zarafin yara.
Olarinde ta bukaci gwamnati, kotuna, jami’an tsaro, jami’o’i, shugabannin addinai da na gargajiya, kafofin watsa labarai da ƙungiyoyin farar hula su haɗa kai wajen yaƙi da cin zarafin mata da yara.
Shi ma Babban Alkalin Jihar Ekiti, Mai Shari’a Lekan Ogunmoye, ya bayyana Bamidele a matsayin mutumin da ya dace ya yi magana kan sabbin ƙalubalen da ke buƙatar gyaran dokoki da tsare-tsaren gwamnati domin kare mata da yara.
A nata jawabin, shugabar FIDA ta Jihar Ekiti, Ayobami Olowoyo-Richards, ta sake jaddada aniyar ƙungiyar na ingantawa, karewa da kuma kiyaye haƙƙoƙin mata da yara.
Ta ce sauye-sauyen da duniya ke fuskanta na haifar da sababbin matsaloli masu sarkakiya da ke barazana ga tsaro, mutunci da haƙƙoƙin mata da yara, don haka akwai buƙatar ci gaba da ƙarfafa dokoki da hukumomin da ke tabbatar da adalci.