
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun ceto wasu makiyaya biyu da aka yi garkuwa da su, tare da kwato dabbobi 520 da aka sace a Jihar Sokoto.
Rundunar ta ce aikin ya gudana ne ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026, a ƙauyen Takasaba da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar.
A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Tamuno Sinivie, ya fitar, ya ce dakarun sun samu sahihan bayanan sirri kan ayyukan ’yan ta’adda a yankin, inda suka garzaya wurin tare da tunkarar maharan.
Sanarwar ta bayyana cewa bayan musayar wuta, maharan sun tsere, suka bar dabbobin da suka sace da kuma mutanen biyu da suka yi garkuwa da su.
An bayyana sunayen mutanen da aka ceto a matsayin Malam Sulaiman, mai shekara 50, da Nasiru Sulaiman, mai shekara 14. Daga bisani, an miƙa su ga hukumomin ƙaramar hukumar Sabon Birni.
A wani aikin daban da ya gudana a ranar, dakarun rundunar sun kuma fatattaki ’yan ta’adda da suka yi musu kwanton ɓauna a kan hanyar Anka–Guruzu a Jihar Zamfara, yayin da suke gudanar da sintiri domin share hanyar daga ayyukan ta’addanci.
A cewar rundunar, sojojin sun mayar da martani da ƙarfin wuta, lamarin da ya tilasta wa maharan janyewa. Sai dai wani soja ya samu raunin harbin bindiga a yayin musayar wutar, kuma an garzaya da shi asibiti. Rundunar ta ce yana cikin kwanciyar hankali.
Rundunar ta ƙara da cewa bayan artabun, dakarun sun tabbatar da tsaron hanyar tare da dawo da zirga-zirga yadda ya kamata.
Kwamandan rundunar Operation FANSAN YAMMA, Manjo-Janar W. B. Idris, ya yaba wa sojojin kan jajircewarsu, tare da umartar su da su ci gaba da matsin lamba kan ’yan ta’adda.
Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro, tare da kira ga jama’a da su riƙa kai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai kan ayyukan da ake zargi.