Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Shekaru Bakwai a Gidan Yari kan Cin Zarafin Yarinya a Yobe

Muhammadu SabiuHausa13 minutes ago



Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu, Jihar Yobe, ta yanke wa wani matashi mai shekara 20, Dauda Umaru, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru bakwai bisa samunsa da laifin shirya da kuma yin jima’i da wata yarinya mai shekara 16.

Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ce ta bayyana hukuncin a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Laraba.

Kotun, wadda Mai Shari’a Aisha Y. Salihu ke jagoranta a ɗakin shari’a na biyu, ta same shi da laifin da ya saɓa wa sashe na 16(1) na Dokar Hana Safarar Mutane ta shekarar 2015, kamar yadda aka yi wa dokar gyara.

Baya ga hukuncin ɗaurin shekaru bakwai, kotun ta umarci wanda aka samu da laifin ya biya jimillar naira miliyan 1.5.

Daga cikin kuɗin, za a biya naira miliyan ɗaya zuwa asusun tallafawa waɗanda suka fuskanci laifuka (Victim Trust Fund), yayin da sauran naira 500,000 za a ba wa wadda abin ya shafa a matsayin diyya.

Kotun ta kuma bayyana cewa rashin biyan kuɗin da aka umarta zai jawo ƙarin zaman gidan yari na tsawon watanni bakwai.

Hukuncin na zuwa ne bayan NAPTIP ta samu nasarar gurfanar da wani mutum mai shekara 27, Hussaini Suleiman, a Jihar Neja, inda aka yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari kan laifin lalata da wata yarinya mai shekara takwas.

Haka kuma, a wani shari’ar daban, kotu ta yanke wa wata mata mai shekara 37, Fatima Sanda, hukuncin shekaru biyu a gidan yari bisa laifin shirya wata yarinya mai shekara 16 domin cin zarafinta ta fuskar jima’i.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...