An Hallaka Mutane Bakwai a Harin ’Yan Bindiga a Jihar Filato



Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari al’ummar Georo da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato, a daren ranar Litinin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa maharan sun afka wa yankin ne da misalin ƙarfe 10:20 na dare, inda suka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin yankin, Bot Silas, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Punch Metro a Jos, ya ce harin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda aka kashe an harbe su ne a shagunan da suke ciki, yayin da wasu kuma aka kai musu hari a wani gidan cin abinci na yankin, inda ake shirya abinci.

Silas ya ƙara da cewa harin na dare ya tilasta wa mazauna yankin tserewa domin tsira da rayukansu.

Da yake mayar da martani kan harin, mai magana da yawun Ƙungiyar Berom Youth Moulders Association (BYM), Rwang Tengwong, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai bayyana shi a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike, su kamo waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Tengwong ya kuma buƙaci jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen kare al’ummomin da ke cikin haɗari, domin bai wa mazauna yankunan damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.

Ya zuwa lokacin da aka kammala tattara rahoton, hukumomin tsaro ba su fitar da sanarwar hukuma kan harin ba.

Wakilin jaridar ya kuma yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, amma ba a same shi ba, domin wayarsa a kashe take.

Join Us
  • Facebook38.5K
  • X Network32.1K
  • Behance56.2K
  • Instagram18.9K

Stay Informed With the Latest & Most Important News

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...