Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Tattaunawar Ƙarin Albashi da NLC, Ta Amince da Tallafin Sufurin ₦70,000 Ga Ma’aikatan Gwamnati

Muhammadu SabiuHausa10 minutes ago



Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) sun amince da kafa kwamitin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi nan take, tare da amincewa da biyan ma’aikata tallafin sufuri na ₦70,000 a kowane wata na tsawon watanni shida, daga Nuwamba 2026.

Sai dai ɓangarorin biyu ba su cimma matsaya kan ranar da za a fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa ba, bayan wani taron sasanci da Ma’aikatar Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi ta Tarayya ta shirya a Abuja.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa yarjejeniyar ta kuma ƙunshi biyan wasu alawus-alawus da ake bin ma’aikatan gwamnati da suka cancanta, a kashi uku na wata-wata, daga Nuwamba 2026.

Haka kuma, an amince da biyan bashin alawus-alawus na watanni 19 da ake bin ma’aikatan lafiya cikin watanni uku, daga Disamba 2026.

Tallafin sufuri da sauran alawus-alawus

A cewar yarjejeniyar da wakilan ɓangarorin biyu suka sanya wa hannu, tallafin sufuri na ₦70,000 zai shafi ma’aikata a dukkan matakan aiki na tsawon watanni shida, daga Nuwamba 2026.

Sai dai yarjejeniyar ba ta yi cikakken bayani kan tsarin biyan tallafin ba, ko kuma ko za a tsawaita shi bayan watanni shida.

Game da alawus-alawus na musamman da ake bin ma’aikatan gwamnati, gwamnati ta amince da biyan su daga ranar 1 ga Mayun 2026, tare da fara biyan bashin da ya taru a kashi uku daidai-wa-daida daga Nuwamba.

Taron ya kuma tattauna batutuwan da suka haɗa da rage farashin man fetur, tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa, walwalar ma’aikatan gwamnati, gyaran tsarin albashin ma’aikatan lafiya na CONHESS, rage haraji da biyan alawus-alawus na haɗari ga ma’aikatan noma.

Sai dai ba a cimma matsaya kan buƙatar rage farashin man fetur ba.

Dangane da rage haraji ga ma’aikata, ɓangarorin sun amince a miƙa batun ga Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa domin nazari, bisa la’akari da cewa haraji batu ne da doka ta tanada.

Haka kuma, an bayyana cewa Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya ta miƙa jerin sunayen ma’aikatan noma da suka cancanci alawus-alawus na haɗari, tare da bayanan kuɗaɗen da ake buƙata, ga Hukumar Kula da Albashi, Kuɗaɗen Shiga da Alawus-alawus ta Ƙasa domin tantancewa.

’Yan fansho sun nemi a biya bashin tallafin

A wani ɓangare na rahoton, Ƙungiyar Masu Fansho ta Ma’aikatan Gwamnati da Kamfanoni Masu zaman Kansu ta Najeriya (FEPPPAN) ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya bayar da umarnin biyan bashin tallafin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur na watanni uku, wanda ya kai ₦75,000 ga kowane mai cin gajiyar tallafin da abin ya shafa.

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a gaggauta daidaita fansho, biyan haƙƙoƙin da ake bin tsofaffin ma’aikata da inganta damar samun kiwon lafiya ga masu karɓar fansho ƙarƙashin tsohon tsarin fansho na Defined Benefit Scheme (DBS).

Waɗannan buƙatu na cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta FEPPPAN a Abuja, mai ɗauke da sa hannun Shugaban Ƙungiyar, Benjamin Amako, da Babban Sakataren ta, Franklin Erinle.

Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan aiwatar da tsarin daidaita fansho, wanda ta ce ya fara aiki a watan Janairun 2026.

Ta buƙaci gwamnati ta fitar da takardar umarnin da ke jagorantar tsarin domin fayyace matsayin Hukumar Kula da Sauyin Tsarin Fansho (PTAD) da kuma bayyana yadda sauyin zai shafi masu karɓar fansho.

FEPPPAN ta jaddada cewa daidaita fansho ya kamata ya haifar da ƙarin kuɗin fansho na wata-wata ga duk masu cin gajiyarsa, tare da yin kira ga hukumomin da abin ya shafa da su bayyana ƙa’idojin tsarin, yadda ake aiwatar da shi da kuma tasirinsa ga tsofaffin ma’aikata.

Yarjejeniyar gwamnati da NLC ta zo ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin ƙwadago ke ƙara matsin lamba domin ɗaukar matakan rage tasirin tsadar rayuwa da inganta ƙarfin sayen kayayyaki na ma’aikata.

Duk da amincewa da kafa kwamitin tattaunawar sabon mafi ƙarancin albashi, har yanzu ba a warware saɓanin ra’ayi kan ranar fara aiwatar da sabon albashin ba.

Join Us
  • Facebook38.5K
  • X Network32.1K
  • Behance56.2K
  • Instagram18.9K

Stay Informed With the Latest & Most Important News

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...