Ƴan Sanda Sun Kama Mutum Mai Shekara 56 Kan Zargin Kona Matarsa Har Lahira



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekara 56, Madarikan Emehinola, bisa zargin cinna wa gidansa wuta da matarsa ke ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

Matar, mai suna Igbagbo Erobe, mai shekara 40, ta mutu ne bayan gobarar da ake zargin mijinta ya haddasa ta kama gidan nasu da ke yankin Igbo-Edu, a Ƙaramar Hukumar Ogun Waterside ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Oluseyi Babaseyi, ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na Abigi ne ranar Lahadi. Ya ce matar ta makale a cikin gidan da ke ci da wuta, ta kasa tsira.

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kama wanda ake zargi tare da fitar da gawar matar.

An ajiye gawar a ɗakin ajiyar gawa domin gudanar da binciken likitoci don gano musabbabin mutuwarta. A halin yanzu, wanda ake zargi yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da aka tura shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), da ke Eleweran, Abeokuta, domin gudanar da cikakken bincike.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Bode Ojajuni, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin ƙwarewa da bin doka. Ya kuma jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci cin zarafin cikin gida ko kisan kai ba, tare da tabbatar da cewa za a binciki zarge-zargen manyan laifuka yadda ya kamata.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...