Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama mutum 17 bisa zargin su da aikata daba da kuma shirya zanga-zanga.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke mutanen ne bayan tattara bayanan sirri. Sai dai ba ta bayyana dalilin shirya zanga-zangar ba.
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa wasu matasa sun taru a kusa da gidan sarki na Nassarawa, inda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado, ke zaune, kafin ‘yan sanda su tarwatsa su da safiyar yau Laraba.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce bayan samun bayanai game da yunkurin zanga-zangar, jami’anta tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun baza jami’ai a wasu wurare a cikin birnin Kano domin hana afkuwar rikici.
Batun masarautar Kano na ci gaba da daukar hankalin jama’a, inda Aminu Ado da Muhammadu Sanusi ke ci gaba da bayyana kansu a matsayin sarakunan Kano.
‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 17 Kan Zargin Daba da Shirya Zanga-Zanga a Kano
