Rundunar ƴan sandan jihar Abia ta ce ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda biyu dake bada kariya ga Ginger Onwusibe ɗan majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar Isiala-Ngwa north da south a majalisar wakilai ta tarayya.
A wata sanarwa ranar Litinin,Maureen Chinaka mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Abia ta ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 08:30 na daren ranar Lahadi.
Ƴan sandan biyu insifecta Dunna Jatau da Insifecta Bala Muhammad na aiki da Base 4 Makurdi na rundunar ƴan sandan dake bawa manyan mutane kariya sun kuma gamu da ajalinsu ne a harin kwanton ɓaunar da aka yi musu.
“Akan hanyarsu kusa da sakatariyar ƙaramar hukumar Umuahia South a Ubakala wasu mutane ɗauke da makamai a cikin mota ƙirar Toyota Corolla suka tare motarsu,” a cewar Chinaka
Chinaka ta ƙara da cewa rundunar ƴan sandan jihar na yin duk mai yiyuwa wajen ganin ta kamo maharan.
Ta ce tuni aka ajiye gawar jami’an ƴan sandan a ɗakin ajiye gawarwaki.