Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta musalta rahoton fashewar bom a birnin Jos

An shiga zaman zullumi a jihar Filato da safiyar ranar Talata bayan da ake fargabar cewa an dasa bam a wata hanya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Alfred Alabo ya  fitar ta ce rundunar ta samu rahoton cewa an dasa wani bam a wani ƙaramin rami akan titin Murtala Muhammad a gefen tsohon ginin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos da safiyar ranar Talata.

Ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar Emmanuel Adesina ya tura kwararru kan kwance  bam ya zuwa yankin kuma bayan sun gudanar da cikakken bincike sun tabbatar da cewa babu komai a wurin.

Sanarwar ta ce kwamshinan ƴan sandan jihar da kuma sauran jami’ansa sun ziyarci domin ganewa idonsu abin da ya faru.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun bayyana cewa mazauna birnin sun ji wata ƙara da ake zargin bam ne ya fashe.

More from this stream

Recomended