Wasu mutane da dama sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na birnin Lagos dama wasu birane a Najeriya.
Zanga-zangar cigaba ce ta zanga-zangar da aka gudanar a cikin watan Agusta domin nuna adawa da matsin rayuwa da ake fama a Najeriya.
Duk da gargadi da suka fuskanta daga jami’an tsaro kan kada a gudanar da zanga-zangar sai gashi mutane sun bazama kan tituna.
Mutane da dama a wurin zanga-zangar sun bayyana damuwarsu kan tsadar rayuwa da ake fama da ita musamman ta kayan abinci da suke nema su gagari da yawa daga cikin ƴan Najeriya.
Wasu daga cikin allunan da masu zanga-zanga ke ɗauke sun yi kira ga gwamnati da ta dawo da tallafin man fetur da kuma na wutar lantarki.