Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun bikin tunawa da ranar da Najeriya ta samu ƴan cin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya..
Olabunmi Tunji-Ojo ministan harkokin cikin gida shi ya sanar da hotun a ranar Asabar a wata sanarwa da babbar sakatariyar dindin ta ma’aikatar, Magdalene Ajani to ta fitar.
Ministan ya yabawa ƴan Najeriya dake da haƙuri da aiki tuƙuru inda ya ƙara da cewa sadaukarwa da suka nuna baza ta tafi haka kawai ba.
Ya kuma jaddada buƙatar ƴan Najeriya da suyi duba kan sadaukarwar da gwarazan da suka kafa ƙasar.
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa baza ayi bikin shagulgula sosai ba na tunawa da ranar saboda halin matsin rayuwa da al’umma suke fuskanta.