Ƙaramin Ministan tsaron, Bello Matawalle, ya ba da umarnin binciko waɗanda suka kashe Alhaji Isa Bawa, Hakimin Gatawa a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, tare da tabbatar cewa an kai su kotu.
Cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Henshaw Ogubike, ya fitar a yau Juma’a, Matawalle ya yi Allah wadai da kisan, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba.
Ya nanata cewa ba za a lamunci irin wannan aika-aika ba, sannan ya umarci babban hafsan tsaro da ya gudanar da cikakken bincike don kamo waɗanda suka aikata wannan ta’addanci.
Matawalle ya yi nuni da cewa batun tsaro na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sa a gaba, kuma tana ba Sojojin Najeriya cikakken goyon baya wajen wannan yaki.