Lamarin tsaro ya tilasta wa gwamnatin Zamfara rufe wasu kasuwannin shanu

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe kasuwannin shanu a kananan hukumomi biyar na jihar nan take.

Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Zamfara, Alhaji Mannir Haidara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Lahadi.

A cewar Haidar, kasuwannin shanun da abin ya shafa sun hada da Danjibga da Kunchin-Kalgo a karamar hukumar Tsafe, da kasuwannin shanu na Bagega da Wuya a karamar hukumar Anka, da Dangulbi da Dansadau a karamar hukumar Maru, Dauran a karamar hukumar Zurmi, da Nasarawar Burkullu a karamar hukumar Bukkuyim.

Ya ce rufe kasuwannin shanun na wucin gadi ya biyo bayan taron kwamitin sulhu ne.

“Wannan wani bangare ne na matakan magance matsalolin tsaro a jihar. Gwamnati ta lura da yadda ake saidawa da lodin shanu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka sace a kasuwannin da abin ya shafa,” in ji Kwamishinan.

Don haka gwamnati ta yi kira ga hukumomin tsaro da hukumar kula da lafiyar dabbobi da kiwo ta jihar da su tabbatar da bin matakan da suka dace.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]