Ƴan fashi sun kashe mutane a Neja

Ƴan bindiga sun kashe manoma 25 tare da yin garkuwa da mata da ‘yan mata da dama daga al’ummomi daban-daban a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Rahotanni sun ce an kai harin ne da misalin karfe biyu na rana a kauyuka biyar.

Alkaluma sun nuna cewa mutane 13 ne suka rasa rayukansu a yankin Kusherki, an kuma kashe wasu 12 a kauyen Gidigori, yayin da wasu da dama suka rasa rayukansu.

Rahotanni sun nuna cewa ayyukan jin ƙai a yankin ya kara lalacewa ne tun daga ranar Laraba, yayin da daruruwan ‘yan gudun hijira da suka hada da mata da kananan yara daga kauyuka daban-daban suka yi tururuwa zuwa Kagara, hedikwatar karamar hukumar Rafi, inda suka bar kauyukan nasu ga ‘yan fashi.

More from this stream

Recomended

Trump Ya Yaba Wa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan abin da ya bayyana a matsayin ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalar tsaro a ƙasar. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Trump ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Tinubu. Ya ce yana yaba wa shugaban […]