Kungiyar MOPPAN ta masu shirya fina-finai karkashin jagorancin,Dr. Ahmad Sarari ta sasanta rikicin da ya barke tsakanin Naziru Sarkin Waka da kuma matan Kannywood.
A wasu kalamai da yayi a baya Naziru ya yi zargin cewa ba a saka yan matan a cikin shirin Fim har sai anyi lalata da su.
Hakan yasa ƙungiyar matan Kannywood ta K-WAN ta bashi wa’adi da ya janye kalamansa ko kuma ta maka shi a kotu.