2023: “Na bar banga saboda abin da ‘yan siyasa ke ba mu ko abinci ba zai saya ba”

.

Wani abu da ake zargin ‘yan siyasa da mayar da hankali a kai a duk lokacin da aka kaɗa gangar siyasa kuma aka fara yaƙin neman zaɓe shi ne amfani da ‘yan bangar siyasa.

‘Yan siyasar dai kan yi amfani da kuɗaɗen a wani lokaci ma ba su taka kara sun karya ba, tare da bai wa matasa ƙwaya don yin amfani da su wajen illata abokan adawa ko kuma tayar da tarzoma a lokutan zaɓe.

To sai dai matasan sun fara karatun ta-nutsu inda aka fara samun wasu suna tuba tare nadamar abin da suka yi a baya, har ma sun shiga fafutukar janyo hankulan takwarorinsu waɗanda har yanzu ba su ritaya daga bangar siyasa ba.

Sagiru Yerima, na ɗaya daga cikin ‘yan bangan da a yanzu suka tuba har ma ya fara jagorantar gangami don tabbatar da ganin an gudanar da zaɓen 2023 ba tare da banga ba a jihar Kano.

A hirarsa da BBC, Sanusi ya ce abin da ya sa ya bar bangar siyasa saboda ya lura a tsawon shekarun da suka yi suna musgunawa mutane, babu wata riba da suka samu haka zalika, a ɓangaren iyayen gidansu, ‘yan siyasa a idan sun tura mota, ta tashi shi kenan sai ta baɗe su da ƙasa.

Wasu ƙarin labarai…

Ya ce babban dalilin da ya sa yake yaƙi da wannan matsala shi ne “babu makoma mai kyau, akwai zalunci da rashin mutunci da amfani da rayuwar ɗan adam don cimma buƙata,”

“Abin da suke bayarwa bai taka kara ya karya ba, yanzu saboda lalacewa har bashi ma ake hayar ‘yan bangar siyasa.” in ji Sagiru Yerima.

Ya bayyana cewa zai yi wahala a iya hana ƴan siyasa ci gaba da shigar da matasa cikin harkar banga, amma hakan a cewar sa, mai yiwuwa ne kuma yana ganin abu mafi dacewa matukar ana son kawar da wannan matsala shi ne, mutanen kirki su riƙa jan matasa masu yin bangar a jiki, don yi musu nasiha.

Sagiru Yerima, wanda magidanci ne yanzu, ya ƙara da cewa yin hakan zai ba su damar haɗa kai da matasan da suka tsinci kansu cikin wannan matsala domin “yaƙar waɗannan gungun miyagun ƴan siyasa.”

Ya ce su kansu matasan da ke bangar suna cikin damuwa game da halin da suka tsinci kansu, kuma wannan ta sa suka kafa wata ƙungiyar yaƙi da bangar siyasa a jihar Kano don ganin irin gudunmawar da za su iya bayarwa.

Ya kuma bayyana girman matsalar ta yadda matasa kan je rumfunan zaɓe domin tada hargitsi a wuraren, inda ya ce hakan na tasiri ne saboda a mafi yawan lokuta jami’an tsaron da ake turawa rumfunan jefa ƙuri’a, ba su da yawan da za su iya samar da cikakken tsaro.

‘Yadda na tsinci kaina a bangar siyasa’

Magidanci Sagiru Yerima ya ce kasancewar “mun tashi a lungunanmu gwargwadon iko mun iya rashin kunya, toh irin wannan damar ƴan siyasa ke amfani da ita sai su dinga neman ya za a yi mu taimaka musu su ci zaɓe.”

Ya ce ƴan siyasar sun kashi gida biyu – akwai masu tunanin yadda za su taimaka wa ƴan banga idan suka ci zaɓe, akwai kuma waɗanda sun fi so su ci gaba da riƙe su a igiyar zato, don su dawwama suna amfani da su don biyan burinsu na siyasa kawai.

“Sau da dama sukan yi amfani da yaudarar cewa zan taimake ka, ana amfani da jahilcin mutane da talaucinsu.” in ji shi.

Gangamin ‘Kano Ba Banga’

Sagiru Yerima ya ce faɗakarwa kaɗai ba ta isa ba wajen daƙile matsalar bangar siyasa, dole ne sai an zauna da matasan da suke bangar saboda “shi ɗan siyasa duk yarjejeniyar da za ka yi da shi, idan lokacin buƙata ya ga ba zai ci ba, toh ina tabbatar maka zai karya ta,”

“Amma su yaran tun da, da su ake amfani, su muke so mu ja a jiki” shi ya sa “muka fito da tsari na kafa ƙungiya mai taken ‘Kano ba Banga”.” in ji shi.

A cewar sa, “kowanne gidan siyasa a Kano, yana da jagoran ƴan bangarsa, haka tsarin yake tafiya.”

Ya ce ƙungiyar za ta ƙunshi wakilci daga jagororin ƴan banga na ƴan siyasa da jami’an hukumar zaɓe da hukumomin tsaro – ƴan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya da malaman addini.

Magidancin ya kuma ce abu ne mai wuya a iya tafiyar da siyasa ba tare da banga ba saboda “an gina siyasar a haka, ba abu ne kuma na yanzu idan zai yiwu,”

“Amma idan shugabanci ya zo na gari, a hankali shi zai janye matasan – kai za ka canza marasa kirkin ciki ka mayar da su masu kirki.” kamar yadda ya faɗa.

Bangar siyasa dai wata matsala ce da ta zama alaƙaƙai a Najeriya musamman a lokutan zaɓe da masana suka ce kan jefa rayuwar masu yinta cikin gagarumin haɗari.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...