Rahotanni sun nuna cewa wasu ƴanbindiga sun yi awon gaba da matafiya 28 daga garin Zak da ke yankin Bashar a ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato.
Wani mazaunin ƙaramar hukumar ya tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, inda ya ce mutanen da aka sace—maza da mata da yara—na kan hanyarsu ta zuwa garin Sabon Layi ne domin halartar taron Maulidi a ranar Lahadi.
Wani mazaunin garin ya kuma bayyana cewa zuwa yanzu babu wani bayani kan inda mutanen da aka sace suke.
A halin da ake ciki, mai magana da yawun ƴansandan ƙasar, SP Alabo Alfred, ya ce rundunar tana bincike kan rahoton faruwar lamarin.
Ƴanbindiga Sun Sace Matafiya 28 a Jihar Filato

