Ƴan takarar shugaban ƙasa a Jamhuriyyar Nijar

Zaben Nijar

Ya rage kusan watan biyar a gudaanr da babban zaben shugaban kasa na 2020 zagayen farko a jumhuriyar Nijar. Zuwa yanzu ‘yan takara 12 ne suka bayyana anniyarsu ta tsayawa zaben shugaban kasar.

Wadannan ‘yan takara na dakon kotun tsarin mulki ta kasa ta tantance su domin su tabbatar da ‘yan takarar da suka dace shiga zaben na 2020.

Duk da cewa kotun ba ta bude lokacin yakin neman zabe ba,to amma wasu ‘yan siyasa sun fantsama yankunan karkara kuma su na ci gaba da gudanar da taruruka da tattaunawa da jama’a.

Daga cikin wadannan ‘yan takara da akwai wadanda suka kasance filin zabe a karo na farko, wasu karon su ne na biyu wasu kuma shi ne na farko, abun da ya sa suka kasance sabbin zuwa a wannan dandali ko kuma filin na takara.

MAHAMANE OUSMANE: A wannan zabe na 2020 zai shiga takarar neman shugaban kasa a karo na bakwai tun lokacin da guguwar dimokradiyya ta shiga jumhuriyar Nijar zuwa yanzu.

A wannan karo zai shiga zaben ne a karkashin jam’iyyar ADR HANKURI CANJI da ke da tuta mai launin kore da fari.

Da akwai wasu ‘yan takarar uku kuma da za suyi zaben na neman kujerar shugaban kasa a karo na uku. Suna hada da SEYNI OUMAROU a karkashin jam’iyar MNSD NASSARA da ABDOULAYE AMADOU TRAORE na jam’iyyar PPNU SAWYI sannan sai HAMA AMADOU na jam’iyar MODEM FA LUMANA.

‘Yan takara masu karancin shekaru

Sai kuma wasu biyu daga cikin ‘yan takarar 12 da suka sanar da tsayawar su zaben shugaban kasar na 2020 -2021 da za su shiga fagen zaben a karo na biyu da suka hada da MAHAMANE MOUMOUNI HAMISSOU a karkashin jam’iyar PJD HAKIKA, da kuma IBRAHIM YACOUBA a karkashin inuwar jam’iyar MPN KIISHIN KAASA.

Bayanan hoto,
Ibrahim Yacouba na jami’yyar MPN KIISHIN KAASA

Wadannan ‘yan takarar biyu na daga cikin matasan ‘yan takarar shugabancin kasar masu karancin shekaru.

Bayan wadannan ‘yan takara shida daga cikin 12 da suka sanar da tsayawa zaben shugaban kasar da akwai wadanda baki ne da suka shigo a karo na farko a wannan dandali.

BAZOUM MOHAMED zai shiga takarar ne a karon farko a karkashin jam’iyar PNDS TARAYYA bayan da jam’iyar ta tsayar da shi a cikin watan Maris 2019.

Bayanan hoto,
Bazoum Muhammad na takara karkashin PNDS Tarayya

SALOU DJIBO tsohon shugaban kasar na mulkin na rukon kwarya bayan juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Mahamadou TANDAJA.

Shi ma zai shiga takarar ne ta ranar 27 ga watan Disamba na 2020 domin neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PJP GENERATION DOUBARA.

ABDOUL KADRI OUMAROU ALFA a karkashin GYYAR ZABE. Karon na farko kenan da ya tsaya takara, kuma a karon farko aka samu irin wannan tsari da wani ayarin jam’iyyun siyasa guda 22 suka tsayar da dan takara daya a zaben shugaban kasa a jumhuriya Nijar.

HABIBOU KADAOURE zai tsaya takara a karon farko a karkashin jam’iyar SDR SABOUWA.

MAHAMADOU ABDOU zai yi takara a karon farko karkashin jam’iyar RANAA sai kuma DJIBRIL BARE a karkahin jam’iyyar UDFP SAWABA.

Zuwa yanzu dai da akwai ‘yan takarar da ake dakon su sanar da tsayawarsu nan ba da jimawa ba. Daga cikin su da akwai CHEIFFOU AMADOU na jam’iyyar RSD GASKIYA da ABOUBAKAR AMADOU CISSE na jam’iyyar UDR TABBAT da TAHIROU GIMBA na jam’iyyar MODEL MA’AIKATA da OMAR HAMIDOU TCHIANA wanda ake kira LADAN TCHIANA da MARIAMA MADAME BAYAR da ALBADE ABOUBA na jam’iyyar JUMHURIYA da SALIM -SALIM ZANGINA da SALOU GOBI da AMADOU SALIFOU da ADEL ROUBET.

Bayanan hoto,
ALBADE ABOUBA na jam’iyyar JUMHURIYA

Wannan dai shi ne karo na farko da za a samun ‘yan takara 20 da ke neman kujerar shugaban kasa a jumhuriyyar Nijar tun soma mulkin dimokaradiya a kasar.

A zaben da ya gabata dai an samu ‘yan takara 15 ne kawai.

Zuwa yanzu dai jumhuriyyar Nijar na da jam’iyyun siyasa 147 da yawan al’ummar kasar ya kai miliyan 21 da kuma ‘yan kasar miliyan tara suka yi rijistar sunayensu domin kada kuri’a a lokacin wannan zabe mai zuwa.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...