‘Ćłan bindiga sun sace fasinjoji daga motoci goma a Zamfara’

A daidai lokacin da aka shiga sabuwar shekarar ta 2022 miladiya, ‘yan bindiga a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da kai farmaki ga al’umma a kan hanyoyin mota da ke cikin jihar.

A cikin wani hari da suka kai da dare zuwa safiyar jiya Asabar kan motocin sufuri, ‘yan bindigan sun kwashi jama’a da dama tare da halaka wasu.

Wata mata da ta auna shekara da ke cikin daya daga cikin motocin da ta rasa abokiyar tafiyarta, ta yi wa BBC karin bayani kamar haka:

“Mun taso daga garin Jibiya da karfe huÉ—u kuma mun isa Funtua da misalin Ć™arfe bakwai da wani abu. Daga nan mun wuto ‘Yankara zuwa garin Kuceri. Ba mu san da su ba saboda suna cikin duhu ne. Kawai sai muka ji Ć™arar harbi a ko’ina.”

Ta ce da direban motar ya ji ana harbinsu, sai ya juya motar zuwa cikin gona, inda ya koma kan titi, amma sai É“arayin suka bi motar har suka harbe tayar motar guda ta baya.

“A lokacin ne wani harsashi da suka harbo ya zoje ni ga kunchi kuma ya wuce ya bi ta cikin kujera, inda ya same ta a kanta.”

Ta ce saboda harbin, “gilashin motar ya watse kuma ya shiga cikin ijiyata ya yanke ni.”

Daga nan ne direban motar ya wuce da su zuwa garin Wanzamai da fasinjojin nasa.

Matar ta ce bayan sun isa Wanzamai sai direban motar ya bukaci jama’a su ba su agaji, “Daga nan sai anka zo da wata mota kuma anka saka ni da waccan wadda anka harba bisa kai domin a kai mu asibiti a ‘Yankara”.

Ta kara da cewa, “Lokacin da munka isa ‘Yankara mun É—auka halbin da anka yi ma ta ga bayanta ne, sai da munka kai asibiti ne sun ka duba kuma sun ka ce ga kai ne anka halbe ta.”

Ta bayyana cewa ana cikin kulawa da ita abokiyar tafiyarta ta cika: “Ana min dressing, kai kafin a gama min dressing ma rai ya yi halinsa.”

Matar ta kuma ce ba motar su barayin su ka fara tarewa ba.

“Sun fara tare wata mota kuma sun halbi wani mutum guda ga kafa cikin motar, inda shi ma ya juyo kuma ya rinka yi ma direban mu alama da hannu cewa akwai matsala amma da yake dare ne takwas da rabi shi yasa bai gani ba.”

Ta bayyana cewa bayan da direban motar da suke ciki ya juya, shi ma ya rika kokarin sanar da wasu direbobin matsalar da ke wurin amma ba su gane ba.

“To sun dai kama wadannan motocin kuma har sun tafi da mutanen da accikin motocin. Sun kama kusan mota goma ciki har da tireloli.”

‘Da naji cewa an harbe ta a baya, na san ta riga ta mutu’

Murtala Aminu shi ne maigidan matar da ta mutu a cikin wannan hari ga kuma abIn da ya ke cewa:

“Zuwa dai karfe shida mun yi waya da ita, kimanin shida da rabi, sai ta ce sun taso har sun wuce Funtua. To bayan na zo gida kuma bayan karfe bakwai, sai aka aiko cewa ana kirana. Har na ki zuwa sai aka ce in tafi mana saboda yana iya yiwuwa abu muhimmi ne.”

Bayan ya isa gidansu sai abokiyar zaman matarsa ta ce an kira waya cewa an harbi Aisha da Jamila. Sai aka ce min a baya aka harbe ta. Ina jin haka sai na ce na san ta rasu.”

Mallam Murtala ya ce daga baya mahaifinsa da wani dan uwansa sun same shi a gida kuma sun tabbatar masa cewa matarsa ta mutu a sanadin harbin da aka yi ma ta a ka.

Ya kuma ce bayan gari ya waye ne aka taho da gawarta kuma aka yi ma ta sutura.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...