Ɗantakar AAC ya kayar da na jam’iyar PDP a zaɓen kansila a jihar Bauchi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi BSIEC ta ayyana, Yunusa Muhammad ɗan takarar jam’iyar AAC a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar kansila a mazaɓar Papa dake ƙaramar hukumar Darazo.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen ranar Asabar a cibiyar tattara sakamakon zabe dake Darazo jami’in tattara sakamakon, Muhammad Abdullahi ya ce ɗantakarar na jam’iyar AAC ya samu kuri’a 1156 inda ya kayar da Ashiru Muhammad Papa na jam’iyar APC da ya samu kuri’a 1053.

Idris Muhammad ɗantakar jam’iyar APC da yazo na uku a zaɓen ya samu kuri’a 290.

Nasarar da ɗantakarar na jam’iyar AAC ya samu ba a cika ganin irinta ba duba da cewa yawancin jami’ya me mulki ce keyin babakere a zaɓukan ƙananan hukumomi.

More from this stream

Recomended