Ƴansanda sun kama barawon babur a Sokoto

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta cafke wani Kabiru Abubakar da ya kware wajen satar babura tare da wasu ‘yan ta’addan.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Talata, an kama wanda ake zargin ne bayan ya saci babur da aka ajiye a asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Sanarwar ta kara da cewa, “An gano babur din ne bayan da aka kama wanda ake zargin, yayin da aka gano mai babur din.”

More from this stream

Recomended