Ƴan sanda sun kama wasu sojan gona biyu

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta ce ta kama ta ce ta kama wasu sojan gona guda biyu Jonathan Yahaya da Muhammad Umar.

Benjamin Hundeyin mai magana da yawun rundunar shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba.

Hundeyin ya ce wani soja mai muƙamin manjo ne dake barikin soja ta shiya ta 81 da ake kira Nigerian Army Provost, Bonny Camp, Victoria Island, Lagos shi ne ya kai mutanen biyu ofishin ƴan sanda na Onikan bayan da aka kama su.

Mai magana da yawun rundunar ya ce  sojoji sun kama ɗaya daga cikin mutanen ne sanye da wandon kakin soja da kuma takalmi a yayin da ɗayan kuma aka kama shi sanye da kakin soja.

“Biyo bayan tambayoyi an gano cewa dukkanin mutanen biyu sojan gona ne. Sun gaza faɗar yadda suka mallaki kakin soja  shine dalilin kama su.” a cewar Hundeyin.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum ɗaya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faɗa tsakanin ƴanbindiga da ƴanbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...