Ƴan fashin daji sun sako mutane 10 bayan da suka ƙarbi miliyan ₦11.5

Ƴan fashin daji sun sako mutane 10 daga cikin 14 da suka yi garkuwa da su makonni uku da suka wuce daga ƙauyen Gefe a ƙaramar hukumar Kujuru ta jihar Kaduna.

Tun da farko rahotanni sun bayyana cewa biyu daga cikin mutanen sun tsere ne bayan daga sansanin da ake   tsare da su lokacin ƴan fashin  suka yi bacci a makon da ya wuce.

Amma a maimakon sakin sauran  mutane 12 bayan da suka ƙarbi kuɗin fansa na naira miliyan ₦11.5 ƴan fashin dajin sun sako mutane 10 ne kawai inda suka dage sai an ciko naira miliyan 4 kudin fansar mutane biyun da suka tsere kafin  su saki mutane biyun dake hannunsu.

Wani daga cikin manyan garin da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa ƴan bindigar sun bayyana haka ne a ranar Talata bayan da suka sako mutanen 10.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur bai ce komai ba kan lamarin bayan da manema labarai suka buƙaci jin ta bakinsa.

More from this stream

Recomended