Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi.
A cewar mazauna ƙauyen gungun ƴan fashin daji da yawansu ya kai 50 sun kai farmaki garin a ranar Juma’a inda suka riƙa harbin kan me uwa da wabi ta ko ina kafin daga bisani maharan su janye ya zuwa cikin daji sai da kashe mutanen garin su 7.
Dagacin ƙauyen Tudun Bici Alhaji Muhammad Mikailu lokacin da yake bayyana halin da suke ciki ga gwamnan jihar Nasir Idris lokacin da ya kai ziyara garin ya roƙe shi da ya tura ƙarin jami’an tsaro ya zuwa garin domin kare faruwar hari makamancin haka anan gaba.
A yayin da yake jajantawa dagacin kan mutuwar mutane 7 a ƙauyen gwamnan ya bada tabbacin cewa za a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa Tudun Bici domin kare mutane da dukikoyinsu daga fuskantar hare-hare.