Ƴan Bindiga Sun Sako Ɗaliban Kuriga

Gwamnan jihar Kaduna,Mallam Uba Sani ya bayyana sakin ɗalibai 137 da aka yi garkuwa da su a garin Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Gwamnan ya sanar da sakin ɗaliban ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter da tsakar daren ranar Asabar.

“Ina sanar da cewa an sako  ɗaliban mu na makarantar Kuriga,”

Uba Sani ya godewa shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu kan yadda ya fifita tsaro da kare ƴan Najeriya musamman ta yadda ya tabbatar da cewa an sako ɗaliban makarantar.

A ranar 7 ga watan Maris ne wasu yan bindiga da ba’asan ko suwaye ba suka yi garkuwa da ɗaliban.

Gwamnan bai bayyana ko an biya kuɗin fansa ba kafin a sako ɗaliban.

More from this stream

Recomended