Wasu ‘yan bindiga sun daki hotunan yadda suka gudanar da sallar Idi-el-Fitr ta bana da sauran bukukuwan da aka yi a fili a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
‘Yan ta’addan, wadanda da alama ba sa cikin wata damuwa, sun taru a filin Idi da ke garin Munhaye da ke Zamfara a ranar Laraba don gudanar da sallar raka’a biyu don nuna karshen azumin Ramadan.
Wata kafa mai suna Zagazola Makama, a shafinta na X, ta bayyana cewa ‘yan fashin sun yi bikin Eid-el-fitr cikin nutsuwa ba tare da wata fargaba ba.
Ana iya ganin ‘yan bindigar da bindigoginsu.
Rahotanni sun nuna cewa sun ɗauki sa’o’i da dama suna karanta Alqur’ani sannan kuma an ga yadda suke murna.