Ƴan bindiga sun saki hotunan yadda suka gudanar da Sallar Idi a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun daki hotunan yadda suka gudanar da sallar Idi-el-Fitr ta bana da sauran bukukuwan da aka yi a fili a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

‘Yan ta’addan, wadanda da alama ba sa cikin wata damuwa, sun taru a filin Idi da ke garin Munhaye da ke Zamfara a ranar Laraba don gudanar da sallar raka’a biyu don nuna karshen azumin Ramadan.

Wata kafa mai suna Zagazola Makama, a shafinta na X, ta bayyana cewa ‘yan fashin sun yi bikin Eid-el-fitr cikin nutsuwa ba tare da wata fargaba ba.

Ana iya ganin ‘yan bindigar da bindigoginsu.

Rahotanni sun nuna cewa sun É—auki sa’o’i da dama suna karanta Alqur’ani sannan kuma an ga yadda suke murna.

More News

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...

NFF ta naÉ—a Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagle

An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle. Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta...

Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ga ma'aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000. Gwamnan...