Ƴan bindiga sun kashe wani basarake da ɗansa a Taraba

Ƴan bindiga sun kashe Tanimu Kunbiya wani basaraken gargajiya tare da ɗansa a garin Chanchangi dake jihar Taraba.

Harin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da mutanen biyu suke kan hanyarsu ta dawowa daga wurin wata jana’iza a garin Takum.

Emmanuel Bello mai magana da yawun gwamnan jihar Agbu Kefas ya ce an yanka marigayin ne.

Ya ƙara da cewa gwamnan jihar ya shiga alhini sosai bayan da ya samu labarin mutuwar.

Bello ya ce gwamnan ya bawa jami’an tsaro umarnin da su gaggauta gudanar da bincike domin gano maharan.

Ya kuma shawarci mutanen Takum da su kwantar da hankali inda ya ci alwashin yin duk mai yiyuwa wajen ganin maharan sun fuskanci hukunci.

More from this stream

Recomended