Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda 4 da wata mai POS a jihar Imo

Wasu ƴan bindiga da ba’asan ko suwaye ba sun kashe jami’an ƴan sanda huɗu a wurin wani shingen binciken ababen hawa dake kan hanyar Owerri-Onitsha a jihar Imo a ranar Litinin.

Shedun gani da ido sun bayyana cewa hari kan ƴan sandan ya faru ne da misalin ƙarfe 06:30 na yamma har ila yau ƴan bindigar  sun kashe wata mace mai sana’ar POS.

Wani mutum da ya sheda harin da ya yi iƙirarin cewa shi mazaunin Ireti ne dake ƙaramar hukumar Owerri-west ta jihar Imo ya ce an jikkata masu wucewa a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa farmakin.

Ƴan bindigar sun farma ƴan sandan ne wurin shingen binciken ababen hawan dake gaban Blossom Otal.

Shima wani da ya shedar faruwar harin ya ce maharan na daga cikin waɗanda suke tabbatar da dokar hana fita ta ranar Litinin da ƴan ƙungiyar IPOB suka saba sakawa a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

More from this stream

Recomended