Zanga-zanga:Tinubu zai wa ƴan Najeriya jawabi ranar Lahadi

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu zai yiwa ƴan Najeriya jawabi a gobe ranar Lahadi kan zanga-zangar matsin rayuwa da ake gudanarwa a sassa daban-daban na ƙasarnan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar ya ce Tinubu zai yi jawabin ne da ƙarfe 7 na safe.

Sanarwar ta shawarci kafafen yaɗa labarai na rediyo da talabijin da su a haɗa da gidan talabijin na NTA da kuma gidan rediyon Najeriya domin su watsa jawabi.

Jawabin na shugaban ƙasar na zuwa ne kwanaki uku da fara gudanar da zanga-zangar  matsi da kuma ƙuncin rayuwa da ya addabi jama’a tun bayan da shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya kama mulki a shekarar da ta wuce.

More from this stream

Recomended