
Gwamnan jihar Niger, Umar Bago ya ce dukkanin makarantun da aka rufe a wasu sassan jihar saboda matsalar tsaro za a sake bude su.
Bago ya fadi haka ne a ranar Juma’a lokacin da ya ziyarci mai martaba sarkin Minna, Umar Bahago a fadarsa.
A kwanakin baya ne wasu da ake zargin yan fashi ne suka kai farmaki kan kashiyan masarautar a Minna.
Gwamnan ya jajantawa sarkin kan faruwar lamarin kana ya bada umarnin kafa shingayen binciken jami’an tsaro a Minna.
“Muna samun nasara akan lamarin kuma wadanda suka aikata haka za su shigo hannu tuni muka bada umarnin kafa shingen bincike a Minna da sauran sassan jihar,” Ya ce.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa baza ta jurewa matasa masu ta da fitina ba ya kara da cewa dole ne bangaren shari’a ya daina bayar da beli ba bisa ka’ida ba da kuma sakin masu laifi.