Yau take Ranar Dimokradiyya a Najeriya

Moshood Abiola

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A yau Laraba ne Shugaban Muhammadu Buhari ke kaddamar da ranar dimokradiyya a karon farko, bayan mayar da ita zuwa bikin 12 ga watan Yuni maimakon 29 ga watan Mayu kamar yadda aka saba a baya.

Bikin ranar 12 ga watan Yuni, na tunawa ne da zaben shugaban Najeriya na 1993, wanda akasarin mutane suka yi imani cewa sanannen dan siyasar kasar marigayi Cif MKO Abiola ne ya yi nasarar ci, kafin gwamnatin mulkin soja ta lokacin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ta soke zaben.

Kafofin labaran Najeriya sun ruwaito cewa, Shugaba Buhari ya sanya hannu a kan kudurin dokar da ya mayar da 29 ga Mayu ranar mika mulki, ita kuma 12 ga Yuni ta kasance ranar hutu don bikin dimokradiyya a kasar.

Sai dai kuma a wani bangaren, wasu tsoffin ‘ya’yan tsohuwar jam’iyyar NRC a jamhuriya ta uku, sun kalubalanci matakin mayar da 12 ga Yuni a matsayin ranar dimokradiyya.

‘Ya’yan tsohuwar jam’iyyar NRC din sun ce ba sa goyon bayan wannan mataki, don a cewarsu dan takararsu Alhaji Bashir Tofa ne ya ci zaben, amma ba Moshood Abiola na SDP ba.

Honorabul Mas’ud Jibril Doguwa shi ne tsohon sakataren jam’iyyar NRC a jihar Kano kuma ya shaida wa BBC cewa ”duk wani dan NRC a Najeriya kwace aka yi masa, ba mu yarda a ce an mayar da wannan ranar dimokradiyya ba.”

Sai dai tun bayan da kasar ta koma turbar dimokradiyya a shekarar 1999, wani babban kalubale da take fuskanta shi ne na tabarbarewar sha’anin tsaro wanda kawo yanzu tana kasa tana dabo kan batun shawo kansa.

Sa’annan kuma cin hanci da rashawa na daya daga cikin abubuwan da suka yi wa kasar katutu inda har shugaban kasar ya ayyana shi a matsayin manyan abubuwan da zai yi yaki da su.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...