‘yankasuwa masu sayen shanu sun fada hannun masu garkuwa da mutane a jihar Taraba

Wasu yanbindiga akan hanyar Wukari zuwa Takum sunyi garkuwa da wasu yan kasuwa masu sayan shanu.
Rohatanni sun nuna cewa yan kasuwar sun fito ne daga garin Ibbi inda suka nufi garin Maraban Baissa a karamar hukumar Donga ranar Asabar domin sayan Shanu lokacin da aka yi garkuwar da su.
Yan kasuwar na dauke da makudan kudade a tare da su lokacin da yan bindigar suka kafa shinge akan hanyar Wukari zuwa Takum a kusa da garin Kofan Amadu suka kuma yi awon gaba da su bayan da suka yi wa matafiya da dama fashi.
Titin wanda shi kadai ne ya hada Wukari da Takum ya dade yana fuskantar barazana daga barayi da kuma masu garkuwa da mutane abin da ya tilastawa mutane da dama kauracewa hanyar a yan kwanakin nan.
Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,DSP David Misal rundunar na iya bakin kokarinta wajen kawo karshen ayyukan masu garkuwa da mutane da kuma barayi da suke addabar mutanen da basu ji ba su gani ba.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...