Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kashe fitaccen ɗan daga da ake nema ruwa a jallo a jihar, Halifa Baba-Beru, wanda ya sanu wajen kai farmaki qa jama’a.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Litinin 22 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 1 na rana, bayan samun kiran gaggawa dangane da wani harin fashi da aka kai a unguwar Gwammaja, karamar hukumar Dala, inda ake zargin Baba-Beru ya jagoranta.
A cewarsa, jami’ai biyu – CPL Abdullahi Ibrahim da S/C Yahaya Sa’idu – sun samu raunuka yayin musayar wuta, haka kuma shugaban ‘yan fashin, Baba-Beru, ya jikkata matuƙa.
Dukkansu an garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda Baba-Beru ya rasu a yayin da ake masa jinya, yayin da jami’an suka samu sauki kuma aka sallame su.
Rundunar ta ce ta kammala bincike kan lamarin, kuma tana ci gaba da farautar sauran abokan aikin Baba-Beru.