Yan Kungiyar IPOB Sun Kashe  Direbobin Manyan Motoci  2 Yan Arewa A Imo

Yan bindiga sun kashe wasu direbobin manyan motoci tare da kone motocinsu a mahadar Ogi dake karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo.

Jami’an hukumar kungiyar direbobi ta NURTW a jihar Imo sun fadawa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Asabar.

Dahiru Musa shugaban kungiyar NURTW a Okigwe wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana cewa sun sanar da jami’an tsaro ciki har da DPO na Okigwe kan faruwar lamarin.

Da yake zayyana yadda lamarin ya faru shugaban ya ce “Wasu da ake zargin mambobin kungiyar IPOB ne sun tsare titi inda suka bude musu wuta a ranar Asabar sun kone motoci dake makare da gari,”

A cewar shugaban ba a jima da faruwar lamarin ba ya sanar da sojoji da kuma yan sanda.

“Sojoji da kuma DPO na Okigwe sun ziyarci wurin da lamarin ya faru. Ni da yan sanda muka dauke gawarwarkin ya zuwa asibiti inda kuma yi musu jana’iza tare binne su a ranar Litinin,”

Da yake karin haske kan faruwar lamarin mai magana da yawun kungiyar NURTW bangaren manyan motoci a tashar Laranto dake Jos, Mahmud Jafaru ya ce motocin na kan hanyarsu ne ta zuwa birnin Fatakwal lokacin da maharan suka farmasu.

Haruna Muhammad da Adamu Ibrahim su ne direbobin da aka kashe a cewar Jafaru.

More from this stream

Recomended